Home Politics Rashin Ingancin Tsarin Yarjejeniya a Siyasar Najeriya Musamman ga Jam’iyar APC

Rashin Ingancin Tsarin Yarjejeniya a Siyasar Najeriya Musamman ga Jam’iyar APC

0
0

Daga Sanata Ahmad Babba Kaita

Kamar yadda nike ji wadansu na kira kan jam’iyar APC ta dauki tsari na yarjejeniya wanda aka fi sani da (Consensus) don fidda gwanaye a zabuka masu tahowa nan gaba, ya zama wajibi in fargar da Jam’iyar APC hatsarin yin hakan a siyasance don jam’iyar ta samu ta tsira da mutuncin ta kuma ba tare da fada irin tarkon da jam’iyar PDP ta fada ba.

Da farko dai Yana da kyau mu farga mu tuna cewa jam’iyar APC ta amshi mulki ne a hannu Jam’iyar PDP a lokacin da kuma PDP take kan gaba wajen tsarin a buge, a take, a wuce. Dogaro da wannan tsarin har yasa mahukunta PDP suka dauka sassaka masu yan Najeriya akayi suyi masu bauta. Ma’ana, suka dauka suna iya yin komai a siyasance yadda suka ga dama ba tare da kula da sharuddan demokaridiyya ba, kuma ba tare da kula da hakkokin al’umma ba.

Hakkan ya haddasa rashin jituwa tsakanin mahukuntan Jam’iya da ya’yanta wanda ya dinga tafarfasa a karkashin kasa ba tare da mahukunta jam’iya sun lura ba; saboda hankalin su ya dauke kuma ya karkata kan tunanin su dogara da karfin mulki suyi abinda suke so. Basu farga da cewa basu da wannan karfin ba har sai da lokaci ya kure; a lokacin zaben 2015 — lokacin da ya’yan jam’iyar masu tasiri suka yi mata bore, suka bar jam’iyar Sannan suka hada karfi da sabuwar Jam’iyar APC don su dauki fansar musgunawar da akayi masu.

Hausawa na cewa ganin buzu a masallaci ya isa yasa tinkiya tsoron Allah. Sannan, duk inda akuyar gaba tasha ruwa, to fa nan ta baya zata sha nata. Ma’ana, duk rashin adalcin da bai bar jam’iyar PDP mai shekaru 16 na mulki a burgaminta ba, to fa ba zai bar Jam’iyar APC mai shekaru 6 ba. Yana da muhimmanci mu zauna da tunanin cewa abinda ya faru a baya na bore irin wanda al’umma sukayi ma PDP, duk da bai taba faruwa ba, an riga an fara kuma yazama makamin maida martanin siyasa a hannun al’umma.

Manufa anan itace, cikin shekaru 6 na mulkin APC dole wasu sun faranta wasu sun kuma bata ma wasu a bangare daya. A dayan bangaren wasu na jira su biya sakayyar farantawar da akayi masu ko su maida martanin batawar da akayi masu da kuri’ar su akan shugabanni da suke kallo idon faranta masu ko bata masu. Kenan, idan APC ta fito da tsari na yarjejeniya tsakanin shugabanni a cikin daki inda talaka baya nan, lallai za ayi tuya a manta da albasa dan akwai yiwuwar duk talaka mai jiran daukar fansa wanda aka hana ya huce haushin shin a zabukan fidda gwanaye, to zai jira ya huce haushin shi kan Jam’iyar gaba daya lokacin zaben gama gari inda babu yarjejeniya.

Tunanin yiwuwar haka yakamata ya zama shine abin damuwar gwamnati da mahukuntan jam’iya tunda ya taba faruwa a baya kadan kamar yadda na tunasar da farko. Rashin adalci, dauki-dora, take-murje da buge-dangwale su suka sa PDP tayi mutuwar fuju’a. Zai zama wauta idan har APC, maimakon tayi amfani da wannan darasin ta wanke goma ta tsoma biyar; taci a huce, ta koma aikata kuskure na da gangan irin wannan.

Babban abin kula shine cewa ita APC sai talaka yafi nuna rashin tausayi wajen daukar fansa akanta Idan ta saki layi bisa dalilin yin alkawarin chanza irin wannan kwamachalar. Wannan abu ne me saukin fahimta. Idan har talaka zai ma PDP zindir, wadda ba tayi mashi alkawarin kare darajar kuri’ar shi ba, me zaisa ya tausaya ma APC da yake da alkawarin haka da ita?

Mafita:

Yanzu lokaci na lallashi, kyautatawa da jaddada amana tsakin al’umma da mu mahukuntan APC. Cikin sa’a da kuma wasu dalilai na bayyane har yanzu akwai APC a cikin zukatan al’ummar Najeriya don kyautatawar da tayi ta bangarori da yawa. To amma kada mu bari wannan ya shiga kan mu har mu dauke shi a matsayin rigakafi ga fushin al’umma wanda zai iya hana su maida raddi idan suka gamsu cewa an hau hanyar komawa inda aka fito. Yana da muhimmanci mu daure muba kanmu shawarar tsayawa kan turbar adalci wadda muka tallata kanmu da ita har aka saye mu.

A ra’ayi na, zamu fi mutunci a idon duniya idan muka tabbatar da tsari na adalci wanda aka gina demokaridiyya bisa, tsari na “Kuri’ar ka, yancin ka”, maimakon tabbatar da tsari na kauda ido aba wasu tsiraru dama su kafa wadanda suka yarda da su ko da kau al’umma bata yarda da su. A wannan gaba da muke Ina ganin yin adalci ga kowa shi yafi komai sauki. A sama da kasa duk mafi yawancin masu mulki sun kawo gabar da tsarin mulki ya haramta masu sake takara Kenan, suna da damar da zasu kauda kai daga abinda zuciyar su ke so su bi abin suka auna suka gamsu shi al’umma ke so.

Haka kuma, a wannan gabar, da yawan mu da muke rike da mukamai zamu fi kowa fahimtar cewa Allah SHI ke bada mulki ga wanda YA so, a inda YA so, a lokacin da YA so. Dan mufi kowa sanin Allah YA karbe gwamnati daga hannun jam’iyar da tatse lalitar kasa kaf sannnan bata jin kunyar yin amfani da karfin soja da dan sanda, da haukan yan banga dan tayi yakin cin zabe. Amma Allah Ya karbe mulkin daga hannunta ya bamu. Kenan, abin ba dabara bace, kuma ba karfin tuwo bane. Zabi ne na Allah wanda ke faruwa yadda YA tsara, lokacin da YA ga dama ba yadda muke so ko yadda muka tsara ba. Shi ribar yin adalcin, ko baka tsira da Kuri’a ba, zaka tsira da mutuncinka har kabar ma bayanka suna da zatayi alfahari dashi.

Allah YA bamu ikon gane adalci da tabbatar dashi, YA kuma tabbatar mana da nasara kan sake samun yardar al’ummar Najeriya don ciyar da Najeriya gaba.

Daga karshe Ina kira da qananan hukumomin jahar katsina 34 da kada su yarda da duk wani tsari da zai tauye masu damar da Allah ya basu a demokradince ta chanja duk wani baren gurbin party ko kuma wani mai riqe da muqami na siyasa irina.

(Consensus)yaudarace da choge karara kuma zagon kasa ne da tauye wa talakka yanci a daidai gabar daya kamata ya yanke ma kanshi hukunci.
Tohh in ba haka ba ya za’ai stakeholders na karamar hukuma kwaya 50 ko kasa da haka su yankewa dubban daruruwan ‘ya ‘yan jam’iyya hukunci?

(0)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *